Moqtada al Sadr yayi tir da 'yan mamaye

Fitaccen malamin nan na Iraki, Muqtada al-Sadr yayi kira ga magoya bayansa da kada su bada kai ga abin da ya bayyana da mamayar Amurka, amma kuma ya yi gargadin cewa a guji daukar makamai.

Ya ce , "har yanzu muna nuna tirjiya, muna adawa da mamayewa ta hanyar amfani da karfi, da al'adunmu da ma duk wani nau'i na kin bada kai. Don haka ku ce ba zamu amince da mamaya ba."

Wannan ne karon farko da yayi jawabi a bainar jama'a tun bayan komawarsa gida daga Iran inda ya shafe shekaru hudu yana gudun hijira na kashin kai.

Al-Sadr ya yi kira ga magoya bayansa da su bada hadin kai ga sabuwar gwamnatin Iraki, inda suke da kujeru bakwai.

Ya kuma yi kira ga mutanen Iraq da su ajiye bambance bambancen da ke tsakaninsu su kaucewa zuba da jini.

Yace samun zaman lafiya abu ne da ya rataya a wuyan dukkan 'yan Iraki.