Shirye-Shiryen Kuru'ar raba gardama a Sudan

Salva Kiir
Image caption Salva Kiir

Jagoran yankin kudancin Sudan Salva Kiir ya ce babu wani zabin da ya wuce na zaman lafiya tsakanin kudanci da arewacin Sudan muhimmanci.

Salva Kiir ya ce zaben raba gadarmar ba shi ne karshe ba, amma yunkuri ne na fara wata sabuwar tafiya. Wannan furuci na sa ya zo ne a jajiberin kuru'ar da za'a kada.

Furucin nasa ya zo ne bayan da rundunar sojin Sudan ta ce 'yan tawaye sun kai hari a wani yanki na kan iyaka tsakanin kudanci da arewaci inda aka kashe 'yan tawaye akalla shidda

An hallaka akalla mutum guda a wani fada da aka yi a yankin Abyei ranar Juma'a, to amma akwai sabani akan wanda ke da alhakin kai harin.