Algeria zata rage kudin abinci

Zanga zangar bakincikin kudin abinci a Algeria
Image caption Gwamnatin Algeria zata rage kudin abinci domin shawo kan zanga zangar da 'yan kasar suke yi kan tashin farashin kudin abincin

Gwamnatin Algeria ta ce zata rage kudin wasu abinci a wani yunkuri don kawo karshen zanga zangar da aka shafe 'yan kwanaki ana yi , wadda kuma tayi sanadiyyar mutuwar mutane akalla uku.

Bayan da ministocin kasar suka kamala wani taron gaggawa, hukumomi sun ce za'a rage kudin harajin da aka dorawa sukari da kuma man gyada.

Wanan shine matakin farko a zahiri da gwamnatin kasar zata dauka domin shawo kan tarzomar data barke a ranar larabar data gabata a birnin Algiers, kan tsadar rayuwa da kuma rashin aikin yi.