Alain Juppe zai ziyarci Niger

Shugabannin Faransa

Gwamnatin Faransa ta sake yin gargadi ga mutanen kasarta da su kauracewa yankin Sahel dake arewacin Afrika, bayan an kashe wasu Faransawa guda biyu wadanda aka sace a jamhuriyar Niger.

Sojojin Faransa sun shiga wani yunkuri na ceto wadannan mutane, amma yunkurin bai yi nasara ba.

Primin Ministan kasar Faransa, Francois Fillon ya umarci Ministan tsaro na Faransar Alain Juppe da ya ziyarci Niamey babban birnin na Niger ranar litinin domin tattaunawa da jami'an kasar.

'Yan Faransar da aka hallaka sun hada da Mr Atoine Delacourt da abokin tafiyarsa, wanda aka ce ya je Niger domin halartar bukin da za'a yi na Mr Atoine a makon gobe tare da wata 'yar Niger.

An yi awon gaba da Faransawan ranar Juma'a da dare daga wani gidan cin abinci a Niamey babban birnin kasar ta Niger.