Rashin aikin yi ya kawo asarar rayuka a Tunisia

Masu zanga zangar bakin cikin rashin aikin yi a Tunisia
Image caption Matsalar rashin aikin yi ya jefa kasar Tunisia cikin tashin hankali, lamarin da ya kaiga asarar rayuka

Rahotanni daga kasar Tunisia sun ce mutane hudu sun mutu a lokacin da jami'an tsaro suka yi artabu da masu zanga zanga kan matsalar rashin aikin yi.

Wadanda suka shaida lamarin da idanun su, sun ce jami'an tsaro sun yi amfani da harsasai domin tarwatsa masu zanga zanga a garin Thala da kuma Kasserine.

Wani dan karamin yaro mai shekaru goma uku na daga cikin mutanen da aka kashe.

Rahotanni sun ce mutuwar yaron ta janyo wata gagarumar zanga zanga a garin na Kasserine

Wakilin BBC ya ce a cewar wadanda suka shaida yadda lamarin ya auku taho- mu- gamar ta faru ne a lokacin faduwar rana a garin Kassareine.

Daga bisani kuma dai sojojin kasar sun shigo garin, domin su tabatar da tsaro a wasu gine ginen gwamnatin kasar