An harbi wata 'yar majalisar dokokin Amurka

Gabrille Gifford
Image caption An harbi 'yar majalisar wakilan Amurka Gabrille Gifford a kanta, a lokacin da take gudanar da wani taro tare da 'yan mazabarta

'Yar majalisar wakilan Amurka karkashin jamiyyar Democrat Gabrille Gifford na gudanar da wani taro a bainar jama'a tare da 'yan mazabarta a wata kasuwa cikin cincirindon jama'a, a lokacin da wani mutum ya bude masu wuta tare da yin amfani da wata bindiga mai sarrafa kanta

An harbi 'yar majalisar a ka kuma harsashin dai ta wuce ne ta kwalkwaluwarta. Likitoci sunyi mata aikin tiyata, sun kuma ce akwai yiwuwar ta tashi.

Sai dai wasu mutun biyar dake halartar taron sun mutu nna take, cikinsu kuwa harda wata 'yar karamar yarinya mai shekaru tara a duniya da kuma wani Alkali. Da dama kuma yanzu haka na can kwance a asibiti cikin wani mawuyacin hali

'Yan sanda sun tsare mutumin da yayi harbin mai shekaru ashirin da biyu

Shugaba obama ya bayyana harbin da cewar wata masifa ce data afkawa kasar bakidaya

Ana dai yiwa 'yar majalisar kallon wata 'yar siyasa da yanzu haka tauraruwarta take haskakawa. Mai shekariu 40 ta kasance a majalisar dokokin Amurka tun shekarar 2007