Tarzoma kan kasuwar hannayen jarin Bangladesh

 Tarzoma kan kasuwar hannayen jarin Bangladesh
Image caption Masu zuba jari na kone-kone a birnin Dhaka na Bangladesh

'Yan sanda sun yi artabu da masu saka jari a Dhaka, babban birnin kasar Bangladesh, bayan da kasuwar hannayen jarin kasar ta fuskanci koma baya mafi muni a cikin kwana guda, tun shekaru 55 da kafa ta.

An dakatar da hada-hada a kasuwar Dhakan, bayan da farashin hannayen jarin yayi kasa da maki dari shidda da sittin - watau kwatankwacin kashi tara da digo ashirin da biyar cikin dari, a kasa da awa guda.

A yanzu 'yan sandan kasar ta Bangladesh sun karbe iko da yankin kasuwanci na birnin Dhaka, inda suka rufe hanyoyin dake kaiwa ga kasuwar hanneyen jarin.

Tun da farko an nemi masu zuba jari da su bar yankin. Sun dai taru ne domin nuna damuwa kan yadda aka rufe kasuwar bayan hannayen jari sun yi mummunar faduwa, amma daga nan sai abubuwa suka fara yamutsewa.

Tashin hankali

Masu zanga-zangar sun kona motoci tare da kunna wuta a kan manyan tituna.

An kuma samu rahotannin tashin hankali a garin Chittagong mai tashar jiragen ruwa, wanda ke da tasa kasuwar hannayen jarin.

Wani dan kasuwa ya shaida wa BBC cewa:

"Na zuba dala dubu 39, amma yanzu sun dawo dala dubu 22, bai kamata haka ya faru ba, ta yaya kasuwa za ta fadi warwas kamar haka, ko akwai matsala a kasuwar muna ci gaba da zuba jari".

Duk da cewa Bangladesh na daga cikin kasashen da suka fi talauci a nahiyar Asia, amma kasuwannin hannayen jarinta biyu sun samu bunkasa a 'yan kwanakin nan, sakamakon bunkasar darajar kamfanonin wayar salula da sauran kamfanonin kasar.

Abin da yasa kasuwar ke jan hankalin dubban kananan masu zuba jari.

Amma a 'yan makonnin da su wuce, jama'a da dama na sayar da hannayen jarinsu, abinda yasa ake rudanin cewa manyan masu zuba jari na janye kudaden bayan sun samu kazamar riba.

Tuni dai Fira Ministan kasar Sheikh Hasina ta umarci da a gudanar da bincike, kuma ministan kudin kasar ya ce nan ba da jimawa ba, gwamnati za ta sayar da wasu kamfanonin da ta mallaka, domin karfafawa kasuwar guiwa.