An tsit na alhini wadanda aka harbe a Amerika

Shugaba Obama da Maidakinsa Michelle
Image caption An tuhumi wani mutum da yin harbin

Shugaba Obama ya jagoranci jama'ar kasar Amurka wajen yin tsit na dan wani lokaci, domin girmama mutanan da aka harba ranar asabar a Arizona.

Mr Obama tare da mai dakinsa, Michelle sun tsaya a kofar fadar White House kansu a sunkuye, yayin da aka buga kararrawar girmama mutane shidan da aka kashe da kuma 'yar majalisar kasar karkashin jam'iyyar Demokrat, Gabrielle Giffords, wadda ta sa mu mummunan rauni.

Likitoci sun ce suna da kyakykyawan fata game da halin da Gabrielle Gifford ke ciki.

An dai tuhumi wanda ake zargi da harbinta da laifin kisan kai na mutanen da suka mutu a lokacin kai harin.