Faransa ta kare yunkurin kwato 'ya'yanta a Nijar

Fira Ministan Faransa, Nicholas Sarkozy

Gwamnatin Faransa ta kare yunkurinta na kwato 'yan kasar biyu da karfin soji wadanda aka kashe bayan da aka sace su a Nijar.

Ministan tsaro, Alain Juppe, wanda ke kan hanyarsa ta zuwa Nijar ya ce, yunkurin ya zama wajibi domin kaucewa zargin cewa Faransa ta daina yaki da ta'addanci.

Mista Juppe ya ce babu tantama kungiyar Al-Qaeda a yammacin kasashen Musulmi da ke Afrika ta Arewa na da hannu cikin sace mutanen.

Harin na ranar Asabar dai shi ne karo na biyu da dakarun Faransa su ka gaza 'yanto 'yan kasar da aka yi garkuwa da su a yankin Sahel a kasa da shekara guda.

Duka-duka Faransawa takwas ne aka cafkesu a Arewacin Afrika daga watan Afrilun bara kuma biyun da aka kashe a baya-bayan nan 'yan kauyen Linselles ne da ke arewacin Faransa, inda al'umar yankin ke bayyana alhininsu.