An yi jana'izar sojojin Nijar da aka kashe

Gidan cin abincin da aka sace Faransawan a Yamai
Image caption Gidan cin abincin da aka sace Faransawan a Yamai

A jamhuriyar Nijar an yi jana'izar wasu jami'an tsaron kasar ukku, jandarmomi, wadanda suka rasa rayukansu, a lokacin farmakin neman kubuto wasu Faransawa biyu, wadanda wasu 'yan bindiga-dadi suka sace a ranar Juma'a da dare, a birnin Yamai.

An gano Faransawan biyu, 'yan shekara ashirin da biyar matattu, a lokacin da ake kokarin kwato su.

Sai dai kungiyoyin farar hula da wasu 'yan Nijar da dama sun nuna rashin gamsuwa da matakin da Faransar ta dauka na shiga farmakin, wanda suke ganin jami'an tsaron Nijar ne kawai ya kamata su tafiyar da shi.

Yanzu haka kuma ministan tsaron Faransar, Alain Juppe, ya isa birnin Yamai, domin ganawa da hukumomin Nijar, da kuma Faransawan da ke zaune a kasar.