Paparoma ya yi kiran da a gyara dokar hukunta sabo a Pakistan

Paparoma Benedict
Image caption Paparoma Benedict

Paparoma Benedict ya yi kira ga gwamnatin Pakistan da ta gyara dokokin da suka shafi sabo, wanda ya hada da hukuncin kisa kan duk wanda ya yi batanci ga addinin Musulunci.

Ya ce ana fakewa da dokar ne domin aikata rashin gaskiya da kai hare- hare kan wasu mabiya addinan da ba su da yawa. Paparoman ya ce kisan gillar da aka yiwa, gwamnan lardin Punjab, wani dan siyasa mai sassaucin ra'ayi a makon jiya saboda ya ki amincewa da dokar da ta shafi aikata sabon, ya nuna bukatar gaggauta yiwa dokar gyara.

Masu aiko da rahotannin sun ce ba sa fai Paparoma ke cewa wata kasa ta canja dokokinta ba.