Zabukan fitar da 'yan takara a Najeriya.

Tutar jam'iyar PDP
Image caption Zabukan PDP ya bar baya da kura

Zabukan fitar da 'yan takarar gwamnoni da jam'iyyar PDP ta gudanar a Najeriya, na nuna cewa wasu gwamnoni da ke kan kujerunsu sun yi nasara.

Gwamnonin sun hada da na jihohin Sokoto, da Kebbi, da Jigawa, da Niger, da Filato da sauransu.

A lokacin da wasu jihohin ba'a kai ga sanar da sakamakon zaben ba, a wasu jihohin zaben ya bar baya da kura.

Jihar Kaduna na daga cikin jihohin da 'yan takara suka yi korafi bayan da aka sanar da gwamnan jihar Mr Patrick Ibrahim Yakowa, a matsayin wanda ya lashe zaben.

'Yan takarar sun yi zargin cewa ba'a bi ka'idojin jami'yyar ba wajen gudanar da zaben,inda kuma suka yi barazanar zuwa kotu don ta yi musu adalci.

Sai dai jami'an gudanar da zaben sun ce sun gudanar da shi cikin adalci, kuma masu korafin na yin hakan ne saboda zafin kayen da suka sha.