Ambaliyar ruwa a Australia

Yadda ruwa ya yi ambaliya a Australia
Image caption Jami'ai sun umarci mutane su bar gidajensu

'Yan sanda sun baiwa mutane umarnin kauracewa wasu unguwanni da ke Brisbane, gari na uku a girma a Australia yayin da ambaliyar ruwa ke gabato babban birnin jihar na Queensland.

An umarci mutane da su tashi daga gidajensu da ke yankuna masu kwari zuwa cibiyoyin agajin gaggawa da ake kakkafawa.

Firimiyar birnin Queensland Anna Bligh, ta bayyana yanayin da cewa wani gagarumin lamari ne mai tsoratarwa, wanda kuma ba a taba tunayin faruwarsa ba.

Wadanda suka shaida faruwar ambaliyar ruwan sun bayyana cewa ta yi kama da Tsunami, inda ake ganin ruwa na ta malala da saurin gaske.

Jami'an 'yan sanda sun ce wata mace da kuma wani yaro sun mutu a garin, bayan da ruwa ya yi awon-gaba da motar da suke ciki.

Kazalika wani mutum da dansa sun rasu bayan ruwa ya ture gidan da suke ciki.

An ceto mutane arba'in ta hanyar yin amfani da jirgen helikofta, bayan da suka haye kan gidajensu don fakewa.