Sabon rikici ya barke a jihar Pilato

Wani rikici da ya sake barkewa a Jos , yankin tsakiyar Nijeriya, ya yi sanadiyyar mutuwar akalla mutane goma sha uku.

Wani mai magana da yawun 'yan sanda, ya ce sun tura jami'ansu zuwa wani kauye na mabiya addinin kirista ne, a yankin Wareng, bayan harin da aka kai da asubahin yau.

Wasu mazauna kauyen sun ce sun ga gawarwakin mutane 13 wadanda ke dauke da raunukan da aka ji musu da adduna da bindigogi.

'Yan sanda sun ce cikin kwanaki ukun da suka wuce sama da mutane talatin ne aka kashe a fadan kabilanci da addini da ake a garin na Jos.