An tura karin jami'an tsaro zuwa jihar Pilato

Babban sifeton 'yan sandan Nijeriya, Hafiz Ringim, ya bada umarnin tura karin 'yan sandan kwantar da tarzoma zuwa jihar Filato mai fama da rikici.

Babban kwamandan runduna ta musamman, mai aikin samar da tsaro a jihar ta Filato, Birgediya Janar Hassan Umaru, ya shaida wa BBC cewa, baya ga 'yan sanda kimanin dari da hamsin da aka tura jihar, akwai kuma karin sojojin da aka ba rundunar, daga Barikin Soja na Rukuba dake jihar ta Filato, domin tabbatar da tsaro a jihar.

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da Rundunar 'yan sandan jihar Filaton ta ce, an kara kashe mutane goma sha takwas, a hare-haren da aka kai a wasu kauyuka dake kewayen birnin Jos.

A bangare guda kuma Wata kungiyar Hausawa 'yan asalin jihar Pilato da ke zaune a Lagos, ta yi kira ga al'ummomin jahar ta Pilato da su rungumi juna ba tare da nuna banbancin addini ko kabilanci ba, domin ciyar da jihar gaba.

Kungiyar tace, rigingimun da ake samu a jihar suna na kara yawaita ne, sakamakon rashin hukunta wadanda ake zargi da hannu a ciki.