An kammala zaben kananan hukumomi a Nijar

Tutar Jamhuriyar Nijar
Image caption Tutar Jamhuriyar Nijar.

A jamhuriyar Niger an kammala zaben kansaloli da na magaddan gari a jihohin kasar takwas.

Mutane fiye da miliyan shidda da rabi ne zasu zabi wakilan al'ummomi kimanin dubu ukku da rabi, a kananan hukumomi sama da dari biyu da sittin.

Zaben na yau, zai share fagen zaben shugaban kasa da na 'yan majalisar dokoki da za a gudanar a karshen wannan watan, a kokarin da ake na mayar da Nijar din bisa tafarkin demokradiyya, bayan juyin mulkin da sojoji suka yi, kusan shekara guda kenan.

Rahotanni sun nuna cewar an fuskanci matsaloli, duk da cewa dai an gudanar da zaben cikin kwanciyar hankali.

Wasu daga cikin matsalolin da aka fuskanta sun hada da na rashin isar kayan aiki da wuri, da ma na rashin kayan aikin a wasu wurare, abinda ya sa ba a gudanar da zaben a wasu yankunan ba.