Zaben kananan hukumomi a Nijar

Tutar Jamhuriyar Nijar
Image caption Tutar Jamhuriyar Nijar.

A jamhuriyar Niger ana can ana gudanarda zaben kansaloli da na magaddan gari a jihohin kasar takwas.

Mutane fiye da miliyan shidda da rabi ne ke zabar wakilan al'ummomi kimanin dubu ukku da rabi, a kananan hukumomi sama da dari biyu da sittin.

Zaben na yau, zai share fagen zaben shugaban kasa da na 'yan majalisar dokoki da za a gudanar a karshen wannan watan, a kokarin da ake na mayar da Nijar din bisa tafarkin demokradiyya, bayan juyin mulkin da sojoji suka yi, kusan shekara guda kenan.

Wasu daga cikin matsalolin da ake kokawa da su sun hada da na rashin isar kayan aiki da wuri, da ma na rashin kayan aikin a wasu wurare.