Tantance 'yan takarar shugabancin kasa a Najeriya

A Najeriya, a yau ne ake sa-ran kwamitin da jam`iyyar PDP mai mulkin kasar ta kafa don tantance masu neman tsayawa takarar shugabancin kasar a karkashin tutarta zai fara aikinsa na tantancewa.

Mutune hudu ne dai ake sa-ran kwamitin zai tantance, wato shugaban kasar Dr Goodluck Jonathan da kuma tsohon mataimakin shugaban kasar Atiku Abubakar, da Madam Sarah Jibril da kuma Sani Dutsin-Ma.

Sai dai yayin da bangaren magoya bayan Goodluck Jonathan ke na`am da kwamitin tantancewar, bangaren magoya bayan Atiku Abubakar fargaba yake bayyanawa sakamakon zargin da yake yi cewar da wuya wasu `yan kwamitin su yi wa dan takararsu adalci.

Zabukan fidda 'yan takarar gwanoni da kuma 'yan majalisun dokokin da jam'iyyar ta PDP ta gudanar dai a baya-bayan nan na cike da rikici.