Jonathan da Atiku sun halarci tantancewa

A yau jam'iyyar PDP mai mulki a Nijeriya ta gana da uku daga cikin masu son jam'iyar ta tsayar da su takarar shugaban kasa.

Shugaba Goodluck Jonathan , da tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar, da kuma Madam Sarh Jibril , duk sun bayyana a gaban kwamitin da jam'iyyar ta kafa domin tantance wadanda zasu tsaya takarar fid-da-gwani da za a gudanar jibi.

Tun kafin fara tantance 'yan takarar, bangaren Atiku Abubakar sun nuna rashin gamsuwa da wasu daga cikin wakilan kwamitin , suna nuna shakku kan ko zasu nuna adalci a aikin nasu.