Wani kwamitin Amurka ya bayar da shawarar tanadar tsaurara dokoki kan harkar mai

Wani kwamiti da fadar gwamnatin Amurka ta kafa domin gudanar da bincike kan malalar man da aka samu a tekun Mexico shekarar da ta gabata, ya bada shawarar aiwatar da wasu jerin sauye sauye masu yawa.

A rahotan sa na karshe, kwamitin ya yi kira da a kafa wata hukuma mai zaman kanta, wadda za ta rika sa ido kan batun samar da kariya, gwamnati ta samar da kwararan matakai da kuma samar da karin kudi tare da horas da hukumomin gwamnatin tarayya.

Rahoton ya maida hankali musamman kan bukatar da ke akwai na kamfanoni su rika gudanar da cikakken bincike game da dukkan hadduran dake tattare da batun gina sabuwar rijiyar mai.

A cewar daya daga cikin shugabannin kwamitin, duka kamfanonin mai da kuma gwamnatin Amirka na da laifi.

Fiye da galan miliyan dari biyu na mai ne ya malala a tekun Mexico, a watan Afrilun da ya wuce, kuma har wa yau ana ci gaba da ganin illar hakan a gabar ruwayen Amurkan