Tantance 'yan takara a jam'iyyar ACN

Tutar jam'iyyar ACN
Image caption ACN ta tantance masu son yin takara

A Najeriya, jam'iyyar adawa ta Action Congress of Nigeria(ACN) ta kammala tantance masu neman tsaya mata takarar shugabancin kasar a zaben da za a gudanar a bana.

Kwamitin tantance 'yan takarar ya ce a ranar 14 ga watan nan ne shugannin jam'iyyar na kasa za su bayyana sakamakon tantancewar da aka yiwa masu son yin takarar.

Alhaji Attahiru Bafarawa na daga cikin wadanda jam'iyyar ta tantance, ya shaidawa BBC cewa ya gamsu da yadda jam'iyyar ta gudanar da aikin tantance 'yan takarar.

Dukkan masu son yin takarar da jam'iyyar ta tantance dai sun fito ne daga yankin arewacin kasar.