Hatsarin mota yayi sanadiyar mutuwar mutane 15 a Ghana

Image caption Taswirar Ghana

A kasar Ghana kalla mutane goma sha biyar ne suka mutu nan take a wani mummunar hadarin mota a wani kauye dake kusa da garin Akomadan dake jihar Ashanti.

Rahotanin dake fitowa daga yankin dai na nuni da cewa wasu manyan mototin bas bas guda biyu ne sukayi taho mu gama ayayin da guda ta nufi arewacin kasar guda kuma take kan hanyar ta zuwa kudancin kasar.

Wa'anda suka mutu a hadarin kuma sun hada da wata mata da goyon ta mai shekaru biyu da haihuwa.

Da dama daga cikin wadanda hatsari ya auku da su, sun samu raunuka kuma suna kwance a asibiti wasunsu rai hannun Allah.

'Barci ne ya kwashi direbobin'

Babban Kwamandan 'yan sanda dake kula da zirga zirgan mototi a wajen wato ASP Albert Odei Quansah ya ce hatsarin na da tada hankali da kuma ban tausayi; "ina jin bacci ne ya kwashe direban motan dake tahiya daga Accra zuwa Tamale dake arewacin kasar inda ya kauce hanya ya doshi hanyar dayar motar da ta fito daga arewacin kasar." ASP Albert Odei Quansah yace to amma sun fara gudanar da bincike don gano ainihin abinda ya janyo hadarin. Sai dai wasu kuma na danganta hadarin da hazo da sukace ya turnuke yanayin wajen. Wa'anda suka gane ma idonsu lamarin dai sun ce dukan mototin biyu na cike makil ne da pasinjoji. A farkon wannan makon ne dai rundunan 'yan sandan kasar dake kula da zirga zirgan mototi wato MTTU ta nuna damuwar ta kan yadda ta ce hadurran mototi ke dada karuwa a cikin kasar a shekarun baya bayan nan. Rundunar 'yan sanda ta ce daga cikin shekara ta 2007 zuwa 2010 sama da mutane dudu shida (6,000) ne suka rasa rayukansu a hadurran mototi da aka samu a sassan kasar daban daban.

Ta ce a matakin da take dauka don shawo kan matsalar zata matsa kaimi wajen wayar ma direbobi kai kan yadda za su kauce ma aukuwar haddura.

Rundunar ta kara da cewa ta kaddamar da wani tsari na nuna ba sani ba sabo ga dukkan direbobin dake tukin ganganci da kuma shan barasa a lokacin da suke tukin mota.