Bincike kan karuwar jama'a a duniya

Rahoto kan karuwar jama'a a duniya

Wani bincike ya yi nuni kan yiwuwar karuwar al'umma a duniya abin da zai haifar da matsaloli da dama.

Rahoton ya ce karuwar jama'a na barazanar jefa biliyoyin mutane cikin halin yunwa, da kishi, da kuma rashin wadatar makamashi.

Rahoton, wanda wata cibiyar injiniyoyi ta Burtaniya ta gabatar, ya ce karuwar al'umma musamman a kasashe masu tasowa, shi ne babban kalubalen da ke fuskantar karni na ashirin da daya, kuma har ya fi sauyin yanayi barazana ga al'umma.

Sai dai kungiyoyin agaji Oxfam da Christian Aid sun soki rahoton saboda gaza bayyana cewa masu arziki a kasashe masu karancin al'umma ne ke haddasa sauyin yanayi ba matalautan da ke zaune a kasashe masu yawan jama'a ba.