Gwamnatin Lebanon ta rushe

Minista Jubran Basil

Gwamnatin gamin gambizar kasar Lebanon ta rushe, bayan da ministoci 11 daga kungiyar Hezbolla da kawayenta da kuma wani minista na hannun daman shugaban kasar suka fice daga gwamnatin hadin kan kasar.

Jubran Basil daya daga cikin ministocin jamiyyun adawar ne ya karanto sanarwar murabus din nasu.

Ya ce: ''Ministocin da suka hadu a nan wajen sun mika takaddar murabus dinsu daga gwamnati.Suna kira ga shugaban kasa da ya gaggauta daukar matakan kafa wata sabuwar gwamnati''.

Ficewar ta su ta biyo bayan binciken da ake gudanarwar game da kisan pira ministan kasar, Rafik Hariri, wanda ake ganin za'a shafawa Hezbollah kashin kaji.