Colombia da Phillipines ma na fuskantar ambaliyar ruwa

Kasar Colombia
Image caption Ana cigaba da fuskantar ambaliyar ruwa a kasashen Colombia da kuma Phillipines

To a kasashen Colombia da Philippines ma ana cigaba da da fuskantar mummunar ambaliyar ruwa.

Masana yanayi dai sun danganta bala'i irin na yanayin da ake fuskanta tun daga bara ga abinda suka kira, La Nina

Wannan dai wani yanayi ne kan kara zafin ruwan tekun dake arewa maso yammacin Australia, kuma hakan ne ke haddasa ruwan sama mai karfin gaske.