EFCC ta kama shugabannin wasu kamfanonin Mai

Farida Waziri
Image caption Farida Waziri

A Najeriya, hukumar yaki da cin hanci da rashawa EFCC ta kame wasu manyan jami'ai dake aiki a wasu manyan kamfanonin mai guda hudu na kasashen waje a wasu sumame da jami'an hukumar suka yi.

Hukumar tace ta kame mutanen ne biyo bayan wasu sabbin bayanai data samu da suka nuna cewa kamfanonin nada hannu a badakalar bada cin hanci ga wasu jami'ai a Najeriya na fiye da dala miliyan 100.

Jami'an da hukumar ke rike da su sun hada da shugabannin kamfanonin Tidewater da Transocean, da kuma Noble Corporation.

A watan jiya gwamnatin Nigeriar ta janye wani kara da ga shigar akan kamfanin Halliburton da kuma shugabannin kamfanin, bayan da aka daidaita inda kamfanin ya biya dollar miliyan 35.