An fara bayyana sakamakon zaben kansiloli a Nijar

Taswirar Jumhuriyar Nijar
Image caption Zaben na Nijar ya ci karo da matsaloli a yankuna da dama.

A Jumhuriyar Nijar, Hukumar zaben kasar ta fara bayyana sakamakon zaben kananan hukumomin da aka gudanar ranar Talata.

Sai dai zaben ya gamu da cikas inda a wurare da dama ba a samu gudanar da shi ba. A wasu wuraren ma har a yau din nan ana gudanar da zaben, kamar a jigar Maradi.

Hukumar zabe ta CENI dai ta ce matsalolin sufuri ne suka janyo jinkiri wajen kai kayyakin zabe zuwa yankunan daban-daban na kasar.

Kansiloli kimanin dubu ukku da rabi ne zaa zaba a kananan hukumomi sama da dari biyu da sittin da ake da su a kasar.

Ana dai kallon zaben na kananan hukumomi a matsayin wani zakaran gwajin sauran zabuka da zaa gudanar a kasar nan gaba a cikin wannan wata.