'Yan sanda sun bude wuta kan masu zanga zanga a Tunis

'Yan sandan Tunisia

Rahotanni daga Tunis, babban birnin Tunisia na cewa jami'an tsaro sun bude a wuta a kan masu zanga zanga. to amma babu wasu rahotanni na mutuwa a sakamakon wannan bude wuta.

Sai dai gabanin haka an kashe mutane hudu, a garin Bizerte dake kusa da birnin na Tunis.

A wasu garuruwan a cikin Tunisia, tashin hankali ya ci gaba,

Rahin aikin yi da tabarbarewar harkokin rayuwa na daga cikin dalilan da suka haddasa wannan tarzoma.

Tarzomar a Tunisia sannu a hankali ta tsananta a cikin wata dayan da ya wuce, kungiyoyin kare hakkin Jama'a sunce mutane fiye da 60 ne jami'an tsaro suka kashe, da yawansu kuma da gangan aka hallakasu.