Tashin hankali ya kazance a Tunisia

Masu tarzoma a Tunisia
Image caption Tarzoma ta tsananta a Tunisia

Rahotanni daga Tunisia sun ce tarzomar da aka kwashe wata guda ana yi ta tsananta duk kuwa da tura dakaru kan titina da kuma kokari da gwamnati ta yi na magance wasu daga cikin korafe- korafen masu zanga-zangar.

Matasa a Tunis babban birnin kasar sun kafsa kan tituna tare da dakarun tsaro a daren jiya sannan sun cunna wuta a kan gine gine, a wata bijire wa dokar hana yawon dare.

A Unguwannin kudancin Birnin an harbe masu zanga zanga 3, kuma an bayar da rahoton karin tashin hankali daga akalla garuruwa 6 a ko'ina cikin kasar.

Majalisar dokokin Tunisia za ta gudanar da wani taron gaggawa a yau domin tattauna rikicin.

Wani dan Nijar mazaunin birnin Tunis, Moussa Mahamadou ya shaidawa sashen Hausa na BBC cewa jamaa na gudanar da al'ammuransu na yau da kullum, amma hankalinsu ya tashi ainun.