Jam'iyyar ACN ta tsaida Malam Nuhu Ribadu a matsayin dan takararta

Malam Nuhu Ribadu
Image caption Malam Nuhu Ribadu

Jam'iyyar ACN a Nigeria ta tsayar da Malam Nuhu Ribadu a matsayin dan takararta na shugaban kasa a zaben da za'a yi a watan Aprilu mai zuwa.

Tun dai gabanin akai ga kada kuru'a, sauran 'yan takara biyu suka janye daga takararsu, abun da ya share fage ga Malam Nuhu Ribadu ya zama dan takarar jam'iyyar ta ACN.

Malam Nuhu Ribadu, wanda tsohon dan sanda ne a Nigeria, shine shugaban farko na hukumar yaki da yiwa tattalin arzikin Nigeria zagon kasa watau EFCC gabanin a sauke shi a shekara ta 2007.