Shugaban Tunisia yayi murabus

Zine al-Abidine Ben Ali
Image caption Zine al-Abidine Ben Ali

Shugaban Tunisia, Zine al-Abidine Ben Ali, yayi murabus bayan jama'ar kasar sun kwashe wata guda suna zanga zanga akan rashin ayyukan yi da kuma tsadar kayayakin abinci.

Praministan kasar ne, Mohammed Ghannouchi, yayi sanarwar a gidan talabijin din gwamnati, inda ya kuma ce a yanzu shi zai ja ragamar mulkin kasar.

A yanzu babu tabbas game da inda tsohon shugaban Tunisiyar yake.

Amma wasu rahotannin da ba a tabbatar ba sun ce ya fice daga kasar.

Murabus din shugaba Ben Ali ya zo jim kadan bayan an kafa dokar ta baci a Tunisiyar, da kuma hana yawon dare, a daidai lokacin da dubban jama'a ke zanga zanga a Tunis, babban birnin kasar.

Akalla mutane 23 ne suka hallaka a tashe tashen hankulan. To amma kungiyoyin kare hakkin jama'a sun ce adadin ya zarta haka nesa ba kusa ba.