Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Naja'atu ba ta da akidar siyasa - in ji Aisha Kaita

Image caption Hajiya Naja'atu ta ce Buhari ya fiye son kansa

Shugabar mata ta sashin Arewa maso Yamma a jam'iyyar adawa ta CPC a Najeriya Hajiya Aisha Kaita ta maida martani kan ikirarin da Hajiya Naja'atu Muhammad ta ACN ta yi cewa janar Muhammad Buhari na CPC ya fiya son san kan sa.

Hajiya Aisha Kaitan ta danganta maganganun da Naja'atun tayi da cewa basu da tushe balle makama.

Jam'iyyun dai biyu da suke wata tattaunawa da niyyar futar da dan takara guda daya a zaben kasar da za'ayi a watan Aprilu mai zuwa.

Sai dai alamu na nuna cewa da wuya shirin nasu ya cimma nasara, ganin yadda aka dau lokaci an kasa cimma matsaya, da kuma yadda kowacce daga jam'iyyun ta futar da wanda zai yi mata takarar shugaban kasar.

Hajiya Aisha Kaitan dai ta shedawa wakilinmu na Kano Yusuf Ibrahim Yakasai cewa, maganar Janar Buharin na da san kai magana ce mara tushe.

A makon da ya wuce a cikin wata hira ta musamman tare da Hajiya Naja'atu Mohammed, wata kusa a Jama'iyar adawa ta ACN a Najeriya, hajiyar ta yi wasu zarge zarge game da abinda ya sa ta rabu da Janar Muhammadu Buhari, dan takarar Jamaiyar CPC.