ANPP zata fidda dan takararta na shugabankasa

Jam'iyyar ANPP a Najeriya
Image caption Jam'iyyar ANPP a Najeriya zata gudanar da babban taronta na kasa inda zata fidda dan takararta na shugabankasa

A Najeriya a yau ne jam'iyyar adawa ta ANPP zata cigaba da gudanar da babban taronta na kasa a dandalin Eagles square a Abuja, babban birnin kasar

Jam'iyyar zata zabi dan takararta na shugaban kasar a zaben kasa baki daya da za'a yi a watan Afrilu mai zuwa.

Masu neman tsayawa takarar shugabancin kasa karkashin jam'iyyar hudu ne dai zasu fafata a wannan zabe, kuma sun hada da gwamnan jihar Kano, Malam Ibrahim Shekarau, da Alhaji Bashir Tofa, Alhaji Dauda Birma da kuma Cif Henry Akande.

A jiya ne dai kwamitin da aka dorawa alhakin tantance 'yan takarar shugaban kasar ya kammala aikinsa, inda ya amince da dukkaninsu.