An fara rajistar masu zabe a Najeriya

Farfesa Attahiru Jega, Shugaban hukumar zaben Najeriya
Image caption Hukumar zaben Najeriya mai zaman kanta zata soma rajistar masu zabe a yau

A Najeriya a ranar Asabar ne Hukumar zabe mai zaman kanta, ta fara yiwa 'yan kasar rijistar samun kantin cancantar kada Kuri'a a zubukan da za'a yi a kasar nan gaba.

Hukumar ta INEC dai za ta dauki makonni biyu tana gabatar da aikin rijistar.

Shugaban Najeriya, Goodluck Jonathan ne, za bude shirin Rajistar a mahaifarsa ta Ogbia, dake jihar Bayelsa, a inda kuma Shugaban Hukumar ta INEC, Farfesa, Attahiru Jega ya jagoranci yi masa rajistar.

Hukumar zabe mai zaman kanta wato INEC ta tabbatar da cewar an shigo da karin na'urori dubu dari da goma cikin kasar, a don haka tace ba za'a ci karo da wata matsala ba.