Fira Ministan Tunisia yayi kira da a tabbatar da doka da oda

Masu zanga zanga a Tunisia
Image caption Fira Ministan kasar Tunisia yace ya umarci sojojin kasar dasu tabbatar da bin doka da kuma oda a cikin kasar

Fira Ministan kasar Tunisia, Muhammed Ghannouchi yayi kira ga jam'ian tsaron kasar su tabbatar da bin doka da oda, 'yan awoyi bayan shugaban kasar, Zainul Abidin Ben Ali ya tsere ya bar kasar sakamakon tarzomar nuna rashin amincewa da mulkinsa.

Fira Ministan yace, ya umarci soja su kawo karshen sace-sace da kuma barnata dukiyoyi

Tserewar Shugaba Ben Ali na kasar Tunisia dai ya bar 'yan kasar cikin wani hali na rashin tabbas da kuma rashin sanin inda suka dosa.

Duk kuwa da dokar hana yawan daren da aka sanya a kasar, sai dai wadanda suka shaida yadda abubuwa suke gudana a fadin kasar da idanunsu sun tabbatar da ganin bata gari suna ta kaiwa da komowa a kan titunan kasar ba tare da ganin koda jami'in dan sanda kwaya daya ba.

An kuma ji kararrakin harbin bindiga a wasu lokutan a tsakiyar garin Tunis, babban birnin kasar.

Yayinda ake kuma jin karar jirage masu saukar ungulu dauke da manya manyan sifiku na magana, suna yin shawagi a sararin samaniyar subhana, tare da yin kira da a kwantar da hankula da kuma jan kunnen mutane na cewar kowa ya koma ya zauna a cikin gidansa.