Shugaban Tunisia ya tsere zuwa kasar Saudiyya

Zine Al Abidene Bin Ali
Image caption Tsohon shugabankasar Tunisia Zine Al Abidene Bin Ali ya tsere zuwa kasar Saudiyya

Kasar Saudi Arabia ta tabbatar da cewa, tsohon shugaban kasar Tunisia, Zainul Abidin Ben Ali da iyalansa sun isa kasar.

Tun farko dai akwai rudani dangane da inda tsohon shugaban Tunisian da iyalansa suka samu mafaka, domin kuwa kasar Faransa tun farko tace, ba zata baiwa tsohon shugaban Tunisian da iyalansa mafaka ba

Wakilin BBC yace tun farko dai Fira Minista Muhammed Ghannouchi fadawa al'ummar kasar Tunisia ta talabijin cewa, tsohon shugaba Ben Ali gudanar da mulki ba, kuma dan haka yayi murabus.

Shugaba Obama na Amurka ya yabawa al'ummar kasar Tunisia saboda abinda ya kira, jajircewarsu akan kwato 'yancinsu a matsayinsu na bil'adama.

Sai dai kuma shugaba Obama yayi kira ga dukkan bangarorin kasar ta Tunisia su guji tada zaune tsaya, kana kuma yayi kira ga shugabannin kasar su shirya sahihin zabe