Gwamna Shekarau ya lashe zaben fidda gwani a ANPP

Jam'iyyar adawa ta ANPP a Najeriya
Image caption Jam'iyyar adawa ta ANPP ta tsaida gwamnan jahar Kano Malam Ibrahim Shekarau a matsayin wanda zai tsaya mata takarar shugabankasa

A Najeriya, jam'iyyar adawa ta ANPP ta zabi gwamnan jihar Kano, Malam Ibrahim Shekararu a matsayin wanda zai tsaya mata takara a zaben shugaban kasa da za a gudanar a watan Afrilun bana.

Gwamnan na Jihar Kano ya samu nasara ne a kan sauran mutane uku da suka nemu nemi jam'iyyar ta tsayar da su takarar a taron da jam'iyyar ta kammala a Abuja.

Malam Ibrahim Shekarau ya samu nasara ne da gagarumin rinjaye da kuri'u dubu hudu da dari da saba'in da takwas a cikin kuri'u dubu biyar da dari uku da goma sha biyar da aka kada a lokacin taron

Wannan ne dai karo na farko da jam'iyyar ta ANPP ta gudanar da zaben fidda gwani, inda masu neman takara da dama suka kara, ba tare da wani ya janye ya bar wa wani ba

Yanzu haka jam'iyyar ta ANPP zata fuskanci jan aikin ganin cewar dan takararta ya samu nasara babban zaben dake tafe