Kalubalen takarar Goodluck Jonathan

Goodluck Jonathan
Image caption Goodluck Jonathan

A Najeriya, kungiyar `yan siyasa dattawan Arewa ta ce za ta ci gaba da fafitikar da take yi, wajen ganin dan bangaren arewacin kasar ne zai tsaya takarar shugabancin kasar a karkashin inuwar jam`iyyar PDP.

A karshen mako ne aka zabi shugaba Goodluck Jonathan a matsayin dan takarar jam`iyyar ta PDP, a lokacin babban taron da jam`iyyar ta yi a Abuja.

Dattawan arewan sun ce taron haramtacce ne, kuma za su ci gaba da kalubalantarsa a kotu, kamar yadda kakakinsu, Alhaji Tanko Yakasai ya shaida wa BBC.

Wannan dai shi ne karon farko da kungiyar ta mai da martani dangane da babban taron jam`iyyar ta PDP.