An soma samun sakamakon kuri'ar raba gardamar Kudancin Sudan

Zaben raba gardama a Sudan
Image caption Fiye da kashi casa'in cikin dari na al'ummar kudancin Sudan dake zaune a kasashen turai sun kada kuri'ar ballewar kudancin Sudan

An soma kidaya kuri'un da aka kada a zaben raba gardama da aka shafe mako guda ana yi a yankin kudancin Sudan.

Fiye da kashi tamanin cikin dari na al'ummar kasar dake yankin kudanci ne suka fito domin kada kuri'arsu a zaben raba gardamar, yayin da kashi hamsin cikin dari suka fito a yankin arewacin kasar.

Sakamakon farko na zaben dai ya nuna cewa, al'ummar yankin kudancin Sudan dake zaune a nahiyar Turai sun zabi ballewa domin kafa kasar kudancin Sudan.

Cikin watan gobe ne dai za'a bada cikakken sakamakon zaben raba gardamar.