Kokarin kafa sabuwar gwamnati a Tunisia

Tankar yaki a Tunisia
Image caption Tankar yaki a Tunisia

Shugabannin siyasa a kasar Tunisia suna tattaunawa kan yadda zasu kafa sabuwar gwamnati, wadda zata cike gurbin da shugaba Ben Ali ya bari, bayan arcewarsa zuwa kasar Saudiyya, sakamakon boren da al'ummar kasar su ka yi.

Praministan kasar, Muhammad Ghannouchi, yana tattaunawa da jam'iyyun adawa domin kafin gwamnatin hadin kan kasa.

Wani kakakin 'yan adawar ya shaidawa BBC cewa, suna tattaunawa ne kan yadda wasu jam'iyyu hudu, ciki har da jam'iyya mai mulki, zasu hada kai na wucin gadi.

Gidan talabijin na kasar ta Tunisia ya ce za a tuhumi tsohon babban jami'in tsaro na fadar shugaban kasa da rura wutar rikici.

Wannan sanarwa ta zo ne bayan da gwamnatin rikon kwaryar kasar ta sanar cewa, zata sassauta dokar hana yawon da ta kafa da sa'o'i hudu.