Cuba ta dan yabawa Obama

Cuba ta dan yabawa Obama
Image caption Wani dan kasar Cuba na shirin karbar kudin da wani dan uwansa ya turo masa daga Amurka

Gwamnatin Cuba ta dan yi marhabun da matakin da shugaban Amurka, Barack Obama ya dauka, na sassauta ka'idojin kai-kawo tsakanin kasashen biyu.

Amma kuma hukumomin Cubar sun yin suka, kan yadda Amurkan ke ci gaba da sawa Cubar takunkumin cinikayya, kusan shekaru hamsin kenan.

Wakilin BBC a Havana, Michael Voss, ya ce a ranar juma'ar da ta gabata, shugaba Barack Obama ya bayar da wata oda kan sassauta takunkumin zirga zirga a tsakanin dalibai da malamai da masu kai ziyara mujami'u a Cuba.

A wani jawabi da ministan harkokin wajen Cuba ya fitar, ya bayyana cewa duk da dai sun yi na'am da yunkurin Amurka na baya-bayan, amma, bai kai abinda aka zata ba, bai kuma yi wani gagarumin sauyi a manufofin Amurkan ba.

Sannan kuma wannan ya bayar da damar aikewa da kudi da yawansu ka iya kaiwa dala dubu biyu a shekara ga duk wani dan Cuba da ba mamban jamiyyar kwaminisanci ba.

Gwamnatin Obama dai ta yi kokarin barin 'Yan Amurkan da suka hada jini da Cuba da su ziyarci 'yan uwansu a gida, ko kuma ma su aika musu da kudade, sai dai kuma an samu gagarumin sauyi ta fuskar al'adu.

A nasa bangaren shugaban kasar Cuba Raul Castro ya fara sakin fursunonin siyasa, sannan kuma yana sake fadada bangaren kamfanoni masu zaman kansu, ta yanda mutane zasu dogara da kansu tare kuma da yin kananan kasuwanci.

Sai dai kuma kawo yanzu, rashin jituwar dake tsakanin wadannan tsoffin abokan kiyayyar tun zamanin yakin cacar baka na nan kamar yanda ya ke.