Jean Claude Duvalier ya koma kasar Haiti

Jean Claude Duvalier
Image caption Tsohon shugabankasar Haiti Jean Claude Duvalier wanda ya shafe shekaru 25 yana gudun hijira a wajen kasar ya komo gida

Tsohon shugaban kasar Haiti, Jean Claude Duvalier ya koma kasar shekaru ashirin da biyar bayan jama'a sun yi boren da ya kifar da gwamnatinsa.

Ya hau karagar mulki ne alokacin da yake da shekaru 19 a duniya bayan daya gaji mahaifinsa

Mista Duvalier, wanda ake yiwa lakabin, Baby Doc, ya isa kasar ne daga Faransa inda yayi zaman gudun hijira.

Shi dai tsohon shugaban kasar dai ya komo Haiti ne a daidai lokacin da ake fuskantar kwan-gaba-kwan baya dangane da zaben shugaban kasar,

'Yan kasar Haitin da dama zasu yi ta raba daya dangane da abinda yake son cimmawa.