Ministan tsaron Isra'ila zai kafa sabuwar jam'iyya

Ministan tsaron Isra'ila Ehud Barak
Image caption Batun tattaunar zaman lafiya da Isra'ila ne kan gaba a rikicin siyasar ta Isra'ila

Ministan tsaron Isra'ila Ehud Barak ya ce zai yi murabus daga shugabancin jam'iyyar Labour domin kafa ta sa jam'iyyar.

Mr Barak yana jagorantar wani bangare ne - mai zaman kansa - wanda ya hada da wasu 'yan majalisar ta Labour hudu.

Masu aiko da rahotanni sun ce matakin zai karfafa gwamnatin hadin gwiwa ta Fira Minista Benjamin Netanyahu, saboda zai bar jam'iyyar Mr Marak ta ci gaba da zama a gwamanti. Labour za ta kada kuri'a kan ko za ta fice daga gwamnatin saboda yadda Mr Netanyahu ya ke fuskantar shirin samar da zaman lafiyar yankin Gabas ta Tsakiya.

Sai dai matakin na Mr Barak na nuna abin da zai faru a watan gobe, yana mai cewa Mr Netanyahu na bada mahimmanci kan shirin zaman lafiya da Falasdinawa, a cewar wakilin BBC Jon Donnison a Jerusalem.