Alassane Ouattara ya yiwa Shugaba Gbagbo tayin kariya

Kasar Ivory Coast
Image caption Mutumin da kasashen duniya suke kallo a matsayin wanda ya lashe zaben shugabankasar Ivory Coast Alassane Oauttara yace babu abinda zai tattauna da Shugaba Gbagbo

Mutumin da kasashen duniya suka dauka a matsayin halartaccen shugaban kasar Ivory Coast, Alassane Oauttara, ya yiwa abokin adawarsa, Laurent Gabgbo tayin kariya, idan har ya sauka daga kan mulki.

Mista Ouattara ya fadawa BBC cewa, ya kada Mista Gbagbo a zaben da ya gabata, dan haka yace babu wani abinda zai tattauna da shi

Wakilin BBC yace tuni dai da ma kungiyar kasashen yammacin Afirka ta ECOWAS ta yi barazanar yin amfani da karfi, idan har Laurent Gbagbo bai mikawa Alassane Outtara mulki ba.