Jam'iyyar MNSD ta ce siyasa ce ta sa aka kai Tandja kurkuku

Tsohon shugaban Nijar, Mamadou Tandja
Image caption Magoya bayan Mamadou Tandja sun ce matakin kai shi kurkuku na da nasaba da siyasa

A jamhuriyar Nijar, 'yan siyasa da ma kungiyoyin kare hakkin bil'adama sun shiga tofa albarkacin bakinsu, game da matakin da gwamnatin mulkin sojan kasar ta dauka, na kai tsohon shugaba Mamadou Tandja gidan yari.

Jam'iyyar tsohon shugaban, MNSD -NASSARA, ta ce matakin na da nasaba da siyasa.

A jiya ne aka kai Malam Mamadou Tanja gidan kason Kollo, mai nisan kilomita talatin da biyar daga birnin Yamai inda da ake tsare da shi a wani kasaitaccen gida da ke cikin fadar shugaban kasa..

Yau watanni goma sha daya kenan da sojoji su ka yiwa Malam Mamadou Tandjan juyin mulki, saboda kiki- kakan siyasar da aka samu a kasar ta Nijar.