Gwamnatin Nijar ta yi wa 'yan takara sassauci

Tutar Nijar
Image caption Ko kotun da ta dakatar da su ta amince da sabon umurnin?

A jamhuriyar Nijar hukumomin kasar sun baiwa jamiyyun siyasar da suka tsayar da 'yan takara a zaben majalisar dokoki karin kwanaki ukku domin sake ajiye takardun yan takararsu wadanda kotun tsarin mulki ta yi watsi da su a karshen mako.

Hakan dai ya biyo bawayn wata muhawara da aka gudanar a makon jiya a karkashin inuwar kungiyar sasanta rikicin siyasa CNDP.

Kotun tsarin mulkin kasar dai ta soke takarar wasu jamiyyu sam daga wasu jihohi baki daya a kan dalillan rashin ingancin takardun yan takarar su .

Sai dai Kuma a karkashin tsarin dokokin jamhuriya ta bakwai , babu wani wurin daukaka kara idan kotun tsarin mulki ta yanke Magana.