Rikicin siyasa ya kunno kai kasar Ireland

Tarayyar Turai
Image caption Ministan kula da harkokin wajen kasar Ireland yace zai kalubalanci Fira Ministan kasar a zaben raba gardamar dake tafe

Gwamnatin Ireland ta rabu gida biyu sakamakon rikicin shugabanci.

Ministan hulda da kasashen waje na Ireland din, Michela Martin ya bayyana aniyarsa ta kalubalantar Fira Ministan kasar, Brian Cowen a zaben raba gardama.

Ministan dai yace, ya mikawa Fira Minista, Cowen takardarsa ta yin murabus daga gwamnati, kuma ba zai zabi Fira Ministan ba a kur'ar da za'a kada a nan gaba.

An dai zargi jam'iyya mai ci da haddasa abinda ya kusa durkusar da bankunan kasar ta Ireland, da kungiyar kasashen Turai ta EU ta ceto.