Gobara ta kama a ofishin PDP dake Sakkwato

Image caption Hedikwatar jam'iyyar PDP a Sakkwato

Wata gobara ta tashi a hedikwatar Jam'iyyar PDP Mai mulki reshen jihar Sakkwato dake arewa maso yammacin Najeria da yammacin ranar lahadi.

Kodayake babu rahoton asarar rai ,wutar wadda ta tashi da misalin karfe shidda na marece ta lashe dukannin hawan farko na ginin inda ofis-ofis din shugabannin jam'iyyar yake.

Har yanzu bata bayyana a fili ko menene ya haddasa wutar ba, wasu daga cikin jami'an jam'iyyar a jihar sun zargi manyan shugabannin ta da cinna wutar da gangan domin kona wasu takardun da za su iya zama shaidar karkata akalar wasu kudaden jam'iyyar kimanin miliyan dari uku da suka yi.

Sai dai Sakataren Jam'iyyar ya musanta hakan inda yace gobarar ta tashi bisa hatsari ne

Wannan dai shine karon farko da irin hakan ke faruwa a jam'iyyar ta PDP a jihar Sakkwato wadda dama ke fama da baraka kuma jama'a sun zura ido domin gani inda wannan guguwar rigimar zata dosa.