An kafa gwamnatin wucingadi a Tunisia

Dan Tunisia rike da tuta
Image caption Har yanzu ana zanga-zanga a kasar

Firaministan Tunisia, Mohammed Ghannouchi, ya bada sanarwar kafa gwamnatin wucin gadi wadda za ta maye gurbin da ya biyo bayan hambarar da Shugaba Ben Ali na Tunisiar.

Ministoci guda shidda sun rike mukamansu, duk kuwa da zanga zangar da jama'a suka fita kan titi suna yi a kan nuna rashin amincewarsu da barin tsaffin ministoci a sabuwar gwamnatin.

Haka nan kuma an baiwa wasu yan adawa su ukku mukaman ministoci a sabuwar gwamnatin.

Tuni dai wasu jam'iyyun adawa suka yi watsi da gwamnatin suna cewar ba a rabu da bukar ba ne an haifi Habu.

Hammal Hammam ke nan, Kakakin Jam'iyyar Labour, inda yake cewar an fadada gwamnatin ce kawai domin a hada da jam'iyyun adawar da aka amicne da su da kuma wasu mutane masu zaman kansu.

To amma wannan bai wuce wata yar kwaskwarima ba kawai.