Badakalar biyan haraji a bankunan Switzerland

Wani tsohon ma'aikacin bankin Switzerland zai bayyana hanyoyin da wasu manyan 'yan siyasa da masu kudi ke bi wurin kaucewa biyan kudaden haraji.

Ma'ikacin Rudolf Elmer zai bankado badakalar ne ta hanyar mika wa shafin kwarmato bayanai na Wikileaks sunaye da kuma lambobin asusun masu ajiya a kasar ta Switzerland.

Shafin na Wikileaks dai zai tabbatar da sahihancin bayanan kafin ya wallafa su a shafin na sa.

Wasu da dama na ganin ba karamar bajinta bace ma'aikacin bakin ya yi.

Wani tsohon kyaftin din soja, wanda ke kula da wani asusu dake da kaddarori wadanda suka kai bilyoyin daloli a wani babban banki a Switzerland, ya ce bashi da kwarin gwiwa game da tsarin ajiye kudi a kasar.

Ya ce bankin ya bada damar kaucewa biyan kudaden haraji amma daga baya ya nemi ya sauya hakan.

Da farko dai bankin ya nemi ya sauya hakan a cikin ayyukansa, amma da hakan ya gagara sai bankin ya nemi ya yi amfani da mahukuntan Amurka da kuma shafin Wikileaks.

Rudolf Elmer zai gurfana a gaban kotu a Switzerland a ranar laraba, saboda keta ka'idodin sirrin bankunan kasar.

Amma kafin a gurfanar da shi zai mika faifan CD guda biyo ga shafin Wikileaks wanda ya kunshi bayanan manyan masu kudi da 'yan siyasa masu kaucewa biyan kudaden haraji a kasashen Amurka da Jamus da kuma Burtaniya.

Ana dai ganin Shugaban shafin na Wikileaks, Julian Assange, ne zai karfi bayanan da tsohon ma'aikacin bankin zai mika a Landan, idan ka'idojin bailinsa sun amince da hakan.

Assange dai na jiran hukunci kotu a Ingila wanda kasar Sweden ta shigar domin tasa keyarsa zuwa kasar domin ya amsa laifuka da su ka danganci kyade.